Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kungiyar ta sanya takunkumin karyar tattalin arziki kan jagoran juyin mulkin kasar ta Guinea Mamady Dambouya kana sun bukaci a gudanar da zabe acikin watanni 6, domin komawa mulkin Demokuradiya, bukatar da wasu masu rajin kare hakkin dan Adama a kasar suke ganin ba za ta yi yu ba.
Ya zuwa yanzu dai jagoran juyin mulkin bai ce uffan ba game da bukatar ta ECOWAS ba. Kasar Guinea na daga cikin kasashen Afirka masu fama da Talauci kuma tana da al-umma miliyan 13. Banda haka ta fuskancin juyin mulki har sau Uku daga lokacin da ta samu ‘yancin kai daga hannun faransa a shekara ta 1958 zuwa yau.
342/